9 Yuni 2016 - 11:58
Kokarin Kauda Ta'addanci a Libiya

Sojojin Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Suna Samun Galaba Akan 'Yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato cewa; sojojin gwamnatin hadin kan kasa ta Libya suna kara samun nasara a cikin garin Sirt da ke hannun 'yan ta'addar kungiyar Isis.

Majiyar tsaron Libya ta ce; Sojojin Kasar Sun kuma kwace wani barikin soja wanda a baya ya ke karkashin ikon kungiyar ta Da'esh, ko Isil.

Tun a cikin watan da ya gabata ne dai sojojin kasar ta Libya da su ke a garin Misratah, su ka fara kai farmaki akan cibiyoyin kungiyar Da'esh. Kuma tun sojojin su ka kwace iko da barikin soja na al-jalidh da kuma yankin Bu Hadi a kusa da Srit.

Tun bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar khaddafi a 2011 ne kasar ta Libya ta fada cikin fadace-fadace a tsakanin kungiyoyin da su ke dauke da makamai, da su ka hada da na 'yan'tadda.288